
A ranar 24 ga wannan wata, rikicin da ke tsakanin kawancen kotuna na Islamic na dakarun rukunin addinai da gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya ya riga ya shiga cikin kwanaki na 6, saboda haka ana kara habaka fagen yakin da ke tsakaninsu, kuma yaki tsakaninsu yana kara tsananta, bangarorin biyu sun yi amfani da manyan bibdigogi na igwa. A ranar 24 ga wannan wata da asuba, kasar Habasha da ke goyon bayan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya ta kai farmaki daga sararin samaniya kan birnin da ke iyakar kasar Somaliya inda dakarun rukunin addinai suka mamaye.
Wadanda aka yi abubuwa a idonsu sun tabbatar da cewa, an riga an kara habaka yakin zuwa wurin da ke kudu maso gabashin Baidoa da yammacinsa da arewacinsa da sauransu, dubban mazaunan wurin sun kauracewa gonansu ,ba su sami damar girbi ba , kuma dabbobin da suke kiwowa sun galabaita, a wasu titunan garuruwa, a ko'ina ana iya ganin gawawakin da ba a binne ba, kididigar da aka yi , an ce, yawan wadanda suka mutu a tsakanin bangarorin biyu da ke gwabzawa da juna ya kai gomai, amma dakarun rukunin addinai da gwamnatin rikon kwarya dukansu sun ce, yawan sojojin da suka mutu bisa sakamakon kashewar da kowanen bangaren ya yi ya kai daruruwa.
1 2 3
|