
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yawan rarar kudi da kasar Sin ke samu daga wajen cinikin waje ya karu da sauri sosai, a shekarar bara a karo na farko yawan rarar kudin ya wuce dalar Amurka biliyan 100. Haka kuma yawan rarar kudi da kasar Sin ta samu daga wajen cinikin waje a tsakanin watan Janairu zuwa Satamba da ya wuce ya kai dalar Amurka biliyan 109.85, wato ke nan ya karu bisa na duk shekarar bara.
Don bunkasa harkokin cinikin waje cikin daidaici, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, tun daga bikin baje koli na birnin Guangzhou na karo na 101, za a mayar da bikin baje-koli na kayayyaki da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasashen waje na Guangzhou da ya zama bikin baje-kolin cinikin waje ta kasar Sin.
Da Malama Wu Yi, mataimakiyar firayim ministar kasar Sin ta tabo magana a kan wannan, sai ta ce, "za a kara kyautata tsarin masana'antu da kayayyaki da ke halartar bikin baje-kolin, yayin da ake kara fitar da kayayyakin kasar zuwa kasashen waje, kuma a yi amfani da bikin wajen kara shigo da kayayyaki daga kasashen waje, a kara shiga da masana'antun kasashen waje da shahararrun samfurorin hajjoji na duniya cikin bikin baje-kolin, don kara ba da taimako wajen gudanar da cinikin waje cikin daidaituwa da inganta hadin guiwar tattalin arziki a tsakanin bangarori da dama." (Halilu) 1 2 3
|