Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-15 15:43:29    
Bikin baje koli na karo na dari na birnin Guangzhou na kasar Sin

cri

Malam Zhang Zhigang, shugaban cibiyar cinikin waje ta kasar Sin yana ganin cewa, bikin baje koli na birnin Guangzhou na farko ya zama alama ce ga bude wa kasashen waje kofar kasar Sin. Ya kara da cewa, "kamata ya yi, a ce, wannan bikin baje-koli na farko wani mataki ne da aka dauka don yin watsi da takunkumi da kasashen yammaci suka kakaba wa sabuwar kasar Sin, kuma karo na farko ke nan da kasar ta bude kofa ga kasashen waje. Yawan kudin musanya da kasar Sin ta samu daga wajen cinikin waje a gun bikin baje-koli na farko na birnin Guangzhou ya wuce kashi 20 cikin dari bisa jimlar kudin musanya da ta samu a duk wancan shekara. Wannan bikin baje-koli mai girma ya samar da kudaden musanya masu daraja da ake bukata wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, sa'an nan kuma ya zama wani abu mai muhimmanci ga manufar kasar game da gudanar da harkokin diplomasiya cikin lumana. "

Bisa kidayar da aka yi, an ce, yawan masana'antu da suka shiga wannan bikin baje koli na birnin Guangzhou da aka fara yinsa a ran 15 ga watan Oktoba da ya wuce ya kai dubu 14, wadanda suka halarci bikin yawansu ya kai misalin dubu 500. Duk wadannan ba a taba ganin irinsa ba a da.

A gun bikin bude wannan bikin baje koli, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya bayyana cewa, bunkasuwar bikin baje-koli na Guangzhou ya nuna hanyar da kasar Sin ta bi wajen bude wa kasashen waje kofa a cikin shekaru 50 da suka wuce. Ya ce, "bikin baje koli na birnin Guangzhou wata alama ce ga manufar kasar Sin game da bude wa kasashen waje kofa. Shirya bikin baje-kolin nan wani babban mataki ne da kasar Sin ta dauka don bude kofarta ga kasashen waje. A cikin shekaru 50 da suka wuce, irin wannan bikin baje-koli da aka shirya ya nuna tarihin sabuwar kasar Sin kan bude wa kasashen waje kofa, kuma ya gwada sabon ci gaba da sabbin nasarori da kasar Sin ta samu wajen yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa da cinikin waje, ka zalika ya shaida cewa, kullum kasar Sin sai kara bude wa kasashen waje kofa take yi."


1  2  3