Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-15 15:43:29    
Bikin baje koli na karo na dari na birnin Guangzhou na kasar Sin

cri

A ran 15 ga watan Oktoba na shekarar nan, an bude bikin baje koli na kayayyaki da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasashen waje da aka shirya a karo na 100 a birnin Guangzhou da ke a kudancin kasar Sin. A cikin shekarun nan 50 da suka wuce, irin wannan bikin baje koli na duniya ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin cinikin waje da bude wa kasashen waje kofa domin kasar Sin. Kuma ya zama alama ce ga manufar kasar Sin game da bude wa kasashen waje kofa.

Bayan da Jamhuriyar Jama'ar Sin ta kafu ba da dadewa ba wato a shekarun 1950, sai kasashen yammaci suka kakaba wa sabuwar kasar Sin takunkumi, amma a wancan lokaci, kasar Sin tana bukatar kudin musanya kwarai don shigo da kayayyakin aikin masana'antu da abubuwan zaman yau da kullum daga kasashen waje. Don yin watsi da takunkumin da kasashen yammaci suka kakaba mata, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawara cewa, tun daga shekarar 1957, za a kan shirya bikin baje koli na birnin Guangzhou sau biyu a ko wace shekara, wato daya a lokacin bazara, saura daya kuma a lokacin kaka.


1  2  3