Kakakin kungiyar WTO malama Boghossian ta kuma ci gaba da bayyana cewa, shigar da kasar Sin cikin kungiyar ya samar da sarari ga sauran mambobin kungiyar. A ganin kungiyar WTO, ba ma kawai kasar Sin ita ce wata mamba mai muhimmanci da ke cikin shiyyar Asiya da tekun Pasific ba, hasali ma ita ce muhimmiyar mambar da ke cikin duk fadin duniya.
Kakakin kwamitin ciniki na kawancen kasashen Turai Atephen Adams ya bayyana cewa, a ganin kawancen kasashen Turai, shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO ya zama babbar nasara ga bangarorinmu biyu . A ganin kasashen Turai, shigar da kasar Sin cikin kungiyar ya bayyana cewa, kasashen Turai za su iya kara shigarsu cikin kasuwannin kasar Sin lami lafiya.
Wani mataimakin wakilin ciniki na kasar Amurka Karan Bhatia shi ma ya bayyana cewa, ko shakka babu, shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO ya kawo fa'ida ga kasar Sin da kasar Amurka duka da kuma ga tsarin cinikayya na duk duniyua.(Halima) 1 2 3
|