Ranar cika shekaru biyar ke nan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO. A cikin shekaru biyar da suka wuce, ko kasar Sin ta zama wata mambar da ke daukar nauyi bisa wuyanta a cikin kungiyar WTO ko kuma ta cika alkawarinta cikin himma da kwazo? Ina ra'ayin gamayyar kasa da kasa kan ayyukan da kasar Sin ta yi bayan shigarta a cikin kungiyar? Game wadannan, wakilin gidan rediyo kasar Sin ya ziyarci wasu jami'ai da masanni na kasar Amurka da na kawancen Turai da sauransu. Ga abubuwan da wakilin ya ruwaito mana:
A birnin Geneva, kakakin kungiyar WTO malama Anoush Der Boghossian ta bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar WTO a shekarar 2001, sai ta kara saurin gyare-gyarenta, ta zartas da wasu dokokin shari'a a jere ta yadda dokokin shari'a nata suke dacewa da ka'idojin kungiyar WTO. Wannan ya sa kasar Sin ta kara bude wa kasashen waje kofa wajen tattalin arziki da cinikayya. Yanzu kasar Sin kasa ce ta uku a duniya wajen shigi da fici. A shekarar 2005, yawan kudaden da kasar Sin ta samu wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ya wuce na kasar Japan. A cikin 'yan shekarun nan da yawa da suka wuce, kasar Sin ta sami manyan sakamako, musamman ma ta yi gyare-gyare bisa babban mataki, kasuwanninta sun bude kofarsu ga cinikin da aka yi a tsakanin kasa da kasa.
1 2 3
|