Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-12 17:32:13    
Gamayyar kasa da kasa sun nuna yabo mai yakini ga kasar Sin saboda ayyukan da ta yi bayan shiga cikin kungiyar WTO

cri

Ayyukan da kasar Sin ta yi su ma sun sami amincewa daga wajen kawancen kasashen Turai. Wani jami'in kula da harkokin watsa labaru na kwamitin ciniki na kawancen Mr Stephen Adams ya bayyana cewa, kasar Sin ta sami ci gaba sosai wajen aiwatar da alkawarin da ta yi a lokacin da ta shiga cikin kungiyar WTO. A fannin nan, da wuya za a bayar da hakikanin adadi, amma ana iya cewa, kasar Sin ta riga ta sauke nauyin da ke kanta a cikin kungiyar .

Wani shehun malami mai suna Anil Gupta ya bayyana cewa, a wasu fannoni, kasar Sin ta sami ci gaba sosai a bayyane, alal misali, kasar Sin ta bude wa duniya kofar kasuwanni masu kananan ciniki da kasuwannin sayar da kayayyaki kai tsaye, amma duk da haka, mun ji cewa, muhimmin ci gaba da ta samu shi ne wajen kare ikon mallakar ilmi. Bisa abubuwan da muka sa ido a kansu, an ce, musamman ma a cikin shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai ga kiyaye ikon mallakar ilmi da kuma aiwatar da dokokin shari'a sosai wajen kiyayen ikon mallakar ilmi.


1  2  3