Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-04 21:46:53    
Kasar Amurka ta yi tsammanin janye sojojinta daga kasar Iraq

cri

Almomi iri iri da aka samu sun bayyana cewa, yanzu, W.Bush wanda ya yi taurin kai wajen rike da ra'ayinsa sosai ya soma yin la'akari da tsara sabuwar manufarsa dangane da kasar Iraq.

Kwanan baya, bayan da W.Bush ya yi shawarwari da firayim ministan kasar Iraq Maliki , ya bayyana cewa, kasar Amurka za ta kara saurin gudanar da harkokin mika hakkin tsaron kai ga sojojin kasar Iraq. A ranar Asabar ta makon jiya, a cikin jawabin da ya yi a cikin shirye-shiryen gidan rediyo na yau da kullum, Mr W.Bush ya bayyana kai tsaye cewa, yana son gyara manyan tsare-tsarensa dangane da kasar Iraq ,ba kara karfafa dabarun tsohon tsarinsa kawai ba .

Wani jami'in da bai fayyace sunansa ba da kuma ya zo daga gwamnatin Bush ya bayyana cewa, shirin W.Bush shi ne don rage yawan sojojin Amurka da ke jibge a kasar Iraq a kai a kai. Da farko ya taimaki kasar Iraq wajen kara daga matsayinta dangane da tsaron kai yadda ya kamata, sa'anan kuma za a janye sojojin Amurka a kai a kai.(Halima)


1  2  3