Yanzu, kungiyar yin nazari kan batun kasar Iraq ta riga ta kammala rahoton bincike kan halin da kasar Iraq ke ciki da manufar kasar Amurka dangane da kasar Iraq, kuma za a bayar da su a ranar lahadi ta makon da muke ciki. Amma kafin 'yan kwanaki da suka wuce, an riga an fayyace shawarar da aka gabatar a cikin rahoton ga kafofin watsa labaru na kasar Amurka.
Kamfanin ABC na kasar Amurka ya bayar da labari cewa, a cikin rahoton, kungiyar yin nazari kan batun kasar Iraq tana ganin cewa, don zaunar da halin da kasar Iraq ke ciki, dole ne a shimfida sojojin Amurka 15 a tsakanin mutanen kasar Iraq dubu. In haka za a yi, to yawan sojojin Amurka da ake bukata zai kai dubu 400, amma yanzu yawansu ya kai dubu 144 kawai. In za a ciyar da sojojin Amurka da yawansu ya kai dubu 400, to kasar Amurka za ta sami matsala wajen harkokin kudi, saboda haka sakamakon da aka samu daga wajen rahoton ya bayyana cewa, dole ne a janye sojoji.
Kungiyar ta kuma gabatar da shawara cewa, ya kamata a taimaki gwamnatin kasar Iraq don kara karfinta, a sa'I daya kuma, a kai a kai ne a janye sojojin Amurka daga kasar Iraq a lokaci lokaci. Idan gwamnatin kasar Iraq ta iya shawo kan halin da ake ciki da sauri da kuma dakatar da ayyukan nuna karfin tuwo, to za a iya jenyawar sojojin Amurka sannu sannu kuma bisa tsari, amma idan gwamnatin kasar Iraq ta sha wahalhalu wajen shawo kan halin da take ciki, to za a janye sojojin Amurka da sauri bisa sanadiyar rage mutuwarsu da jin raunukansu. Kungiyar ta kuma bayyana cewa, idan gwamnatin tsakiya ta kasar Iraq ba ta iya ba da amfaninta tare da samun sakamako ba , to kowane aikin da sojojin Amurka za su yi ba ya da amfani.
1 2 3
|