Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-04 21:46:53    
Kasar Amurka ta yi tsammanin janye sojojinta daga kasar Iraq

cri

A ranar 3 ga wannan wata, a cikin shirye-shiryen da kamfanin CNN na kasar Amurka ya shirya, mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka wajen harkokin tsaron kasa Mr Stephen Hadley ya fayyace cewa, shugaban kasar Amurka W.Bush zai yi la'akari sosai da shawarar da Mr Donald H. Rumsfeld ya gabatar, kuma ya gane sosai cewa, dole ne kasar Amurka ta gyara manufarta dangane da kasar Iraq.

An fayyace cewa, Mr Rumsfeld ya gabatar da shawararsa ne a cikin wata takardar fahimtar juna da ya yi kafin ya yi shelar murabus daga mukaminsa a watan jiya. A cikin takardar fahimtar juna, an amince cewa, yanzu, sojojin Amurka sun sami cikas wajen aiwatar da ayyukansu a kasar Iraq, yanzu kuma lokaci ya yi da za a samu daidaituwa sosai a kan manufar Amurka . Takardar ta kuma gabatar da shawara cewa, ya kamata a janye sojojin Amurka daga inda suke yin saukin shan farmakin da aka yi musu, sa'anan kuma su zama wata rundunar sojojin ko ta kwana. A takaice dai ne, ana soma yin shiri sosai don janye sojojin Amurka daga kasar Iraq. Mr Hadley ya bayyana cewa, Mr W.Bush yana yin la'akari da wadannan shawarwari, kuma ya yi fatan za a soma janye sojojin Amurka daga kasar Iraq. Amma kafin ya tsai da kudurin, Mr W.Bush yana bukatar saurarar ra'ayoyi sosai daga wajen bangarori daban daban kan manufarsa ta Iraq, ciki har da shawarar da kungiyar yin nazari kan batun Iraq ta majalisun kasar Amurka ta gabatar .

1  2  3