Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 17:15:48    
Kasar Sin tana kokari sosai wajen shawo kan cutar kanjamau

cri

Kasar Sin ita ma ta sami babban taimako daga wajen gamayyar kasa da kasa a fannin shawo kan cutar kanjamau, yawan kudin taimako da gamayyar kasa da kasa suka bai mata ya karu daga kimanin dalar Amurka miliyan 30 a shekarar 2003 zuwa dalar Amurka miliyan 60 a shekarar nan. Madam Mariam Khan, mataimakiyar wakiliyar ofishin asusuwan yawan mutane na majalisar dinkin duniya da ke a kasar Sin ta bayyana cewa, "tun daga shekarar 2002, kungiyar kayyadde yawan haihuwa ta kasar Sin ta yi nasarar yin amfani da kwaroron roba a ko ina cikin birnin Liuzhou na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon aiwatar da harkokin kanta. Asusun yawan mutanen nan zai ci gaba da aiwatar da harkokin yin amfani da kwaroron roba a ko ina cikin gundumomi biyar na kasar Sin, inda cutar kanjamau ke yaduwa sosai."

Ta hanyar bai wa kasar Sin gudummuwa, gamayyar kasa da kasa sun kuma samar da kudade da sabon ra'ayi da daraba da fasaha, sun taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan cutar kanjamaru a kasar Sin.

Amma ya zuwa yanzu, kasar Sin tana fuskatar kalubale mai yawa wajen shawo kan cutar kanjamau, wadanda suka hada da shawo kan cutar kanjamau da makaurata ke yi, da raina da jama'a ke nuna wa masu cutar kanjamau da sauransu. Sabo da haka, wajibi ne, nan gaba kasar Sin za ta kara kokari wajen gudanar da harkokin shawo kan cutar kanjamau, kuma ta samar da kyawawan gurabe ga yin aikin shawo kan cutar a fannin labaru da fasaha da kuma ra'ayoyin jama'a da sauransu. (Halilu)


1  2  3