Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 17:15:48    
Kasar Sin tana kokari sosai wajen shawo kan cutar kanjamau

cri

Ran 1 ga wata rana ce ta yaki da cutar kanjamau ta duniya ta 19. A kwanakin nan, an yi amfani da damar da aka samu don tunawa da ranar nan, wajen gudanar da harkoki iri-iri na ba da ilmi dangane da yaki da cutar a wurare daban daban na kasar Sin. A lokacin da ake gudanar da harkokin, wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, kullum gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci ga ayyukan shawo kan cutar kanjamaru, kuma ta sami kyakkyawan sakamako. Amma duk da haka a halin yanzu, kasar Sin tana fuskantar kalubale mai yawa a fannin shawo kan cutar, nan gaba, wajibi ne, za ta kara kokari wajen gudanar da aikin shawo kan cutar.

Yawan mutane da ke dauke da kwayoyin cutar HIV da masu cutar HIV ya kai dubu 650 a yanzu a kasar Sin. Halin da ake ciki a kasar dangane da yaduwar cutar ya kai intaha. Malam Wang Longde, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai ga aikin shawo kan cutar kanjamau, kuma ta dauki tsauraran matakai da yawa. Ya bayyana cewa, "a shekarar nan, kasar Sin ta fitar da dokar shawo kan cutar kanjamau, wato ke nan za ta aiwatar da ayyukan shawo kan cutar bisa dokar, haka kuma ta tsara shirin daukar matakin shawo kan cutar kamjamau don wasu shekaru masu zuwa, inda ta kara bayyana manufar ayyukan da matakai da za ta dauka bisa manyan tsare-tsare."


1  2  3