Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 17:15:48    
Kasar Sin tana kokari sosai wajen shawo kan cutar kanjamau

cri

Wannan jami'i ya kara da cewa, yanzu, ana nan ana aiwatar da matakai daban daban wajen shawo kan cutar kanjamau a kasar Sin sannu a hankali. Ya zuwa watan jiya, kasar Sin ta kafa dakunan ba da maganin da ake kira METHADONE a Turance da yawansu ya wuce 300, yawan masu shan miyagun kwayoyi da aka ba su maganin ya kai kimanin dubu 30. Ban da wannan kuma kasar Sin ta aiwatar da manufofi da kyau dangane da ba da magani ga masu cutar kanjamau ba tare da biyan ko anini ba, da sauransu, kuma ta yi ta daga matsayin ilmin jama'a kan cutar kanjamau ta hanyar yin farfagandar shawo kan cutar.

Gwamnatin kasar Sin tana kokarin hadin kanta da kasashe daban daban wajen shawo kan cutar kanjamau. Yanzu, kasar Sin ta riga ta dauki alkawarin ba da gudummuwar kudin dalar Amurka miliyan 10 ga "asusun duniya ta yaki da cutar kanjamau da ta tibi da zazzabin cizon sauro", sa'an nan ta aiwtar da wasu ayyuka cikin hadin guiwarta da sauran kasashe, kuma tana kokari sosai wajen yin shawarwari tare da kasashen Afrika a wannan fanni.


1  2  3