Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 15:26:22    
Ake bunkasa masana'antun kera kayayyakin aiki cikin sauri a arewa maso gabashin kasar Sin

cri

Bisa kokarin da aka yi ta yi ba tare da kasala ba, jimlar kudi da aka samu daga wajen samar da kayayyaki wato GDP a larduna uku na arewa maso gabashin kasar Sin ta karu da kashi 12.3 cikin dari a shekarar bara. Yawan kudin jari da 'yan kasuwa na kasashen waje suka zuba a wuraren nan kai tsaye shi ma ya karu da kashi 89.5 cikin dari, wato ke nan ya fi matsakaicin yawan nan na kasar sosai.

An ci gajiyar masana'antun kera kayayyakin aiki sosai wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin arewa maso gabashin kasar Sin a cikin shekarun nan da suka wuce. A kwanakin baya, an taba shirya wani bikin baje koli na duniya na masana'antun kera kayayyakin aiki na kasar Sin a birnin Shenyang da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Da Malam Song Qi, mataimakin magajin gari na Shenyang ya tabo magana a kan wannan bikin baje-koli, sai ya bayyana cewa, "masana'antun kera kayayyakin aiki wadanda suka kasance a sahon gaba a duk kasar Sin sun shiga cikin bikin baje kolin nan da aka shirya a birnin Shenyang tare da kayayyakinsu. Sabo da haka za mu gano gibi da ke a tsakanin masana'antun kasarmu da takwaransu na kasashen waje, sa'an nan kuma za mu dauki tsauraran matakai wajen cim ma matsayinsu, ta yadda za a kara daga matsayin kasarmu na kera kayayyakin aiki."

An ruwaito cewa, nan gaba, gwamnatin kasar Sin za ta fitar da manufofi don kara nuna gatanci wajen farfado da tsohon sansanin masana'antu na arewa maso gabashin kasar Sin, sabo da haka ana da kyakkyawar makoma wajen bunkasa masana'antun kera kayayyakin aiki na wurare da ke arewa maso gabashin kasar Sin.(Halilu)


1  2  3