Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 15:26:22    
Ake bunkasa masana'antun kera kayayyakin aiki cikin sauri a arewa maso gabashin kasar Sin

cri

A shekarar 2004, an fara gudanar da manyan tsare-tsare don farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin a fannoni daban daban. A cikin shekarun nan biyu da suka wuce, an sami sakamako mai kyau wajen bunkasa tattalin arzikin yankin nan, musamman ma an bunkasa masana'antun kera kayayyakin aiki cikin sauri.

Tun can zamanin da, yankin arewa maso gabashin kasar Sin sansanin manyan masana'antu ne a kasar Sin. Masana'antunsa na kera kayayyakin aiki yana kan matsayi mai muhimmaci na tattalin arzikin duk kasar Sin. Amma bayan shekarun 1970, wannan tsohon sansanin masana'antu ya sami koma baya ainun, idan an kwatanta shi da na wuraren kudu maso gabashin kasar Sin da ke bakin teku. Malam Zhang Guobao, shugaban ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin mai kula da harkokin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar ya bayyana cewa, "tsarin raya tattalin arziki bisa shiri ya kawo tasiri sosai ga tsohon sansanin masana'antu na arewa maso gabashin kasar Sin, sabo da haka tsarin masana'antun nan tsari ne na bai daya, sa'an nan tsarin mallakarsu ma tsari ne na bai daya, wato gwamnatin kasar na da ikon tafiyar da harkokin tattalin arziki, ka zalika sansanin masana'antun nan ba su bude kofarsu ga kasashen waje sosai ba, idan an kwatanta su da biranen kudancin kasar da ke a bakin teku. "


1  2  3