Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 15:26:22    
Ake bunkasa masana'antun kera kayayyakin aiki cikin sauri a arewa maso gabashin kasar Sin

cri

A shekarar 2002, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, za ta ba da taimako ga tsohon sansanin masana'antu na arewa maso gabashin kasar Sin don gaggauta gyare-gyare da za a yi a kansu. Kuma a shekarar 2004, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta kafa hukumar kula da harkokin arewa maso gabashin kasar, nan take an fara yin ayyuka wurjanjan don neman farfado da wurare da ke arewa maso gabashin kasar Sin.

A sakamakon sauye-sauyen tsare-tsare da riba mai yawa da aka kara samu daga wajen masana'antun, ma'aikatan masana'antun arewa maso gabashin kasar Sin an kara musu gwarin guiwa don farfado da tsohon sanananin masana'antunsu. Malam Zhang Guobao, shugaban ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin mai kula da harkokin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar ya kara da cewa,

"a ganina, abin da ya fi sauya a wurare da ke arewa maso gabashin kasar Sin, shi ne ra'ayoyin mutane da tunaninsu sun sauya. Haka kuma tsare-tsaren wuraren nan ma sun sauya daga asalinsa."


1  2  3