Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-29 17:06:46    
Bayani a kan Hongkong

cri

Bayan da aka komo da Hongkong, Hongkong ta kara bude tsarin kudinta, kuma tushen tattalin arzikinta da dokokinta ya kara ingantuwa, mutanen Hongkong sun karfafa imaninsu ga makomar Hongkong.

Yanzu akwai mutanen da yawansu ya kai kimanin miliyan 6 da dubu 700 a Hongkong, kuma dallar Hongkong 100 sun tashi daya da kudin Sin yuan 100.7.

Sai kuma game da shin ko da gaske ne Hongkong na da sojojinsu daban da na babban yankin kasar Sin? To, kamar yadda muka bayyana muku a baya, Hongkong ba ta da ikon gudanar da harkokin tsaro da na diplomasiyya, sabo da haka, Hongkong ba ta da sojojinsa daban da na babban yankin kasar Sin, kuma rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin da gwamnatin kasar Sin ta girke a Hongkong su ne suke kula da harkokin tsaron Hongkong. Rundunar tana da sojojin kasa da na ruwa da kuma na sama, kuma tana jan damara mai kyau. Sojojin da ke girke a Hongkong suna da nauyin kula da tsaron yankin musamman na Hongkong, bisa bukatar gwamnatin yankin musamman na Hongkong da kuma amincewar gwamnatin kasar Sin, sojojin suna iya taimaka wa gwamnatin yankin musamman na Hongkong wajen kiyaye tsaron zaman al'umma da ba da agaji.(Lubabatu)


1  2  3