Da karfe 12 da minti 4, Jiang Zemin, tsohon shugaban kasar Sin ya sanar da cewa, bisa sanarwar hadin kan Sin da Burtaniya a kan batun Hongkong, gwamnatocin kasashen biyu sun yi bikin komo da Hongkong bisa lokacin da aka tsai da, kuma mun sanar da maido da mulki a kan Hongkong, kuma gwamnatin yankin musamman ta Hongkong na jamhuriyar jama'ar Sin ta kafu a hukunce.
Mr.Jiang Zemin ya ce,
'za mu rike marigayi Deng Xiaoping a zukatanmu, wanda ya gabatar da manufar 'kasa daya amma tsarin mulki guda biyu'. Daidai ne bisa wannan babbar manufa, muka daidaita batun Hongkong ta hanyar diplomasiyya kuma cikin nasara, kuma mun cimma burin komo da Hongkong a kasar mahaifarta. Bayan da Hongkong ta komo, gwamnatin kasar Sin za ta tsaya tsayin daka a kan bin manufar 'kasa daya amma tsarin mulki guda biyu', kuma mutanen Hongkong su ne za su tafiyar da harkokin kansu, tsarin zaman al'umma da tattalin arziki da hanyoyin zaman rayuwa da Hongkong ke bi a da ba za su sauya ba, kuma yawancin muhimman dokokinsa ba za su sauya ba.'
Bisa manufar 'kasa daya amma tsarin mulki guda biyu', bayan da aka komo da Hongkong, ban da harkokin tsaro da diplomasiyya, Hongkong tana da babban ikon tafiyar da harkokin kanta, wato tana da ikon tafiyar da harkokin mulkinta da 'yancin kafa doka da kuma 'yancin gudanar da shari'a da cikakken ikon yanke hukunci a fannin shari'a, kuma bisa doka, mazaunan Hongkong suna da 'yanci a fannoni daban daban. Yankin musamman na Hongkong zai bunkasa tsarin dimokuradiyya da ya dace da hakikanin halin da yake ciki sannu a hankali.
1 2 3
|