A cikin shirinmu na yau, za mu amsa tambayar da malam Sanusi Isah daga birnin Keffi na jihar Nasarawa ta tarayyar Nijeriya ya yi mana, a cikin sakon Email da ya aiko mana, ya ce, Hongkong wani yanki ne na kasar Sin, wanda ya yi fice a harkar kasuwanci da sufurin jiragen sama da na ruwa a duniya. Shin yaushe ne yankin Hongkong ya komo karkashin mulkin kasar Sin, ka san cewa a da can yana karkashin kulawar kasar Burtaniya, kuma mutane nawa suke da zama a wannan yanki mai muhimmanci ga tattalin arzikin duniya? Yaya dararjar kudin Hongkong yake da kudin babban yankin kasar Sin? Shin wai ko da gaske ne Hongkong tana da sojojinsu daban da na babban yankin kasar Sin?
To, masu sauraro, yanzu bari mu dan bayyana muku yankin Hongkong na kasar Sin, don amsa tambayar malam Sanusi Isah da kuma kara fadakar da masu sauraronmu a kan Hongkong.
A karfe sha biyu na safiyar ranar 1 ga watan Yuli na shekara ta 1997, a cikin kide-kiden taken kasar Sin ne, aka daga tutar jamhuriyar jama'ar kasar Sin da kuma tutar yankin musamman na Hongkong a yankin Hongkong, lallai ne, Hongkong ta komo kasar mahaifarta a karshe bayan sauye-sauyen da ta sami a cikin shekaru fiye da 100 da suka wuce, kuma daga nan, gwamnatin kasar Sin ta maido da mulki a kan yankin Hongkong.
1 2 3
|