
Taron wasannin motsa jiki na Asiya ya sha bamban da taron wasannin Olympic saboda an kafa wasu gasannin da suka fi samun karbuwa a kasashe da yankunan Asiya, amma ba su shiga cikin taron wasannin Olympic ba. Kungiyar kasar Sin ta shirya sosai domin wadannan gasanni, bisa ka'idar shiga gasa cikin himma da kwazo da kuma yin takara a tsanake. Mr. Duan ya ce,'Ko da yake an kafa gasannin da ba na taron wasannin Olympic ba da yawa a cikin taron wasannin motsa jiki na Asiya na Doha, amma kasarmu za ta yi iyakacin kokari wajen shiga cikinsu, za mu bayyana ra'ayin kasar Sin na shiga cikin gasa cikin himma da kwazo, bugu da kari kuma, za mu kara yin koyi da kuma mu'amala da yankin Asiya. Za mu kyautata halayen da 'yan wasanmu ke ciki da kuma karfafa kwarewarsu ta yin takara a jere yadda ya kamata, don neman gwada gwanintarmu a cikin wadannan gasanni a wannan gami.'
Mr. Duan ya ci gaba da cewa, 'yan wasan kasar Sin suna sa ran alheri domin yin fintikau a Doha, da horar da kansu domin taron wasannin Olympic na Beijing, a sa'i daya kuma, za su isar da zumuncin da jama'ar Sin ke nuna wa jama'ar kasashe da yankunan Asiya.(Tasallah) 1 2 3
|