Taron wasannin motsa jiki na Asiya na Doha gaggarumin taron wasannin motsa jiki na duniya ne da kwamitin wasan Olympic na kasar Sin ta aika da babbar kungiya a karo na karshe kafin taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Mataimakin shugaban kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin kuma mataimakin shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin Duan Shijie ya yi bayanin cewa,'Kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin za ta shiga taron wasannin motsa jiki na Asiya da za a yi Doha a matsayin mai masaukin taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 da kuma taron wasannin motsa jiki na Asiya da za a yi a birnin Guangzhou a shekarar 2010, shi ya sa za ta jawo hankali sosai. Dukan 'yan wasa da malamai masu horars da wasanni da ma'aikata za su yi kokari don samun maki mai kyau, sa'an nan kuma, za su girmama 'yan takara da alkalin wasa da al'adun gargajiya da na kabilun wurin da kuma addininsu.'
An ba da karin haske cewa, 'yan wasa matasa sun sami rinjaye a cikin wannan kungiyar kasar Sin, a cikin dukan 'yan wasa 647, 'yan wasa 167 ne kawai suka taba shiga gasannin taron wasannin Olympic na Athens, wasu 176 kuma sun taba shiga taron wasannin motsa jiki na Asiya da aka yi a Busan. A maimakon haka, 'yan wasa fiye da 400 ba su taba shiga cikin manyan gasannin duniya ba. Mr. Duan ya yi bayani kan wannan cewa,'Saboda yawancin kungiyoyinmu sun shiga cikin manyan gasannin duniya, kamar su gasannin fid da gwani na duniya da kuma gasannin cin kofin duniya da kuma gasannin cancantar shiga taron wasannin Olympic na shekarar 2008 daya bayan daya a wannan shekara, kuma taron wasannin motsa jiki na Asiya na Doha yana kusa da lokacin hunturu, yawancin kungiyoyinmu suna hutu, shi ya sa muka aika da matasa da su shiga cikin wasu gasannin taron wasannin Olympic. Manyan dalilan da ya sa haka su ne da farko, muna gaggauta horar da matasa don share fage ga taron wasannin Olympic na shekarar 2008, na biyu kuma, wasu 'yan wasa kwararru suna bukatar hutu kadan saboda sun shiga manyan gasanni da yawa a shekarar bana.'
1 2 3
|