Za a yi taron wasannin motsa jiki na Asiya a karo na 15 tun daga ran 1 zuwa ran 15 ga watan Disamba na wannan shekara a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar.
Ran 17 ga wata, kasar Sin ta sanar da kafa kungiyar wakilan 'yan wasa don shiga wannan taron wasannin motsa jiki mafi muhimmanci a nahiyar Asiya. Kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin tana kunshe ne da mutane fiye da 900, a cikinsu kuma akwai 'yan wasa fiye da 600. Taron wasannin motsa jiki na Asiya da za a yi a Doha taron wasannin motsa jiki na Asiya ne na 9 da kwamitin wasan Olympic na kasar Sin ta aika da 'yan wasa don shiga. Tun bayan taron wasannin motsa jiki na Asiya da aka yi a New Delhi a shekarar 1982, kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin ta zama ta farko a cikin jerin kasashe da yankuna a fannin samun lambobin zinariya har sau 6. Shugaban kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin Liu Peng ya bayyana cewa, neman zama ta farko wajen samun lambobin zinariya a karo na 7 a jere wani makasudi ne da kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da shi a gun taron wasannin motsa jiki na Asiya da za a yi a Doha. Wani makasudi daban da kasar Sin za ta nemi tabbatar da shi shi ne horar da 'yan wasa domin taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008.
1 2 3
|