A shekarar 1992, Kungiyar Kula da Ilmi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi kwarin Jiuzhaigou a kan takardar sunayen wuraren tarihi na hallita na duniya tare da wani wurin shakatawa daban wato shiyyar wurare masu ni'ima ta Huanglong, wadda nisan da ke tsakaninta da kwarin Jiuzhaigou ya kai misalin kilomita 130. Ta yi suna ne domin ruwa.
Masu yawon shakatawa suna iya jin dadin kallon ruwa daga kan tsaunuka. A cikin kwarin, akwai wani tudu mai launin rawaya-rawaya mai tsawon misalin kilomita 4 ya yi kama da wani dragon iri na kasar Sin mai launi zinariya, wanda ya kwanta a tsakanin bishiyoyi da tsaunukan kankara mai taushi. A kan wannan rawayan tudu akwai kananan tabkuna manya da kanana fiye da 3,000, sun ba da haske sosai saboda rana. Tabkin da ke wurin mafi tsayi shi ne tabki mai suna Wucai, wanda yake hade da kananan tabkuna misalin 700, sun nuna launuka iri daban daban domin hasken rana, ma iya cewa, su ainihi na shiyyar Huanglong.(Tasallah) 1 2 3 4
|