Kwarin Jiuzhaigou ya ba mutane mamaki saboda ruwansa Karste, ruwa rai ne a gare shi. Akwai tabkuna fiye da 100 manya da kanana masu launuka iri daban daban a cikin wannan kwari, 'yan kabilar Zang na wurin suna kiransu 'ya'ya maza na teku. Ruwan da ke cikin wadannan tabkuna na da tsabta sosai, har ma an iya ganin kananan duwatsu da ciyayin ruwa da kuma matattun rassan itatuwa a gindin tabkunan. Launukan ruwan suna da iri daban daban, kamar shudi da kore da kuma rawaya. Babban dalilin da ya sa haka shi ne domin tsarin kasa na wannan kwari shi ne iri na Karst. Mr. Morishita Sadamasa, dan kasar Japan ya yaba wa tabkuna sosai, ya ce,
'Na taba kallon wurare masu ni'ima na kwarin Jiuzhaigou a kan TV a kasarmu, amma bayan ganin wurare masu ni'ima a nan, ina ganin cewa, sun fi kyan gani bisa wadanda na taba gani a kan TV. Akwai irin wadannan tabkuna a kasarmu, duk da haka wadanda ke cikin kwarin Jiuzhaigou sun fi kyaun gani.'
1 2 3 4
|