Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-28 17:28:39    
Ziyarar Aljannar da ke duniyarmu---kai ziyara ga kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong

cri

Ban da ruwan da ke cikin tabkunan kuma, an samu magangarar ruwa 17 a cikin kwarin Jiuzhaigou. Ba su da tsayi sosai, amma suna da fadi sosai, idan aka hango daga nisa, sai ka ce labule na ruwa mai fadi ya rufe hayi duka, yana da kyaun gani, kuma ya ba mutane mamaki sosai.

A ganin mazaunen wurin 'yan kabilar Zang, wurin wuri ne mai tsarki, wanda Allah ya ba su, wata budurwa wai ita Yinamanhong, 'yar kabilar Zang ta ce,

'Mu 'yan kabilar Zang mun gaskanta cewa, dukan aububuwa suna da rayuka, tsaunuka da bishiyoyi da kuma ruwa Allah ne ya ba mu. Tilas ne mutane su kiyaye su, a maimakon lalace su. Tsoffi sun gaya wa 'ya'yansu, kada su wanke tufafi a cikin kogi, ko kuma ajiye abubuwa masu kazanta a cikin kogi.'

Har zuwa yanzu 'yan kabilar Zang suna ci gaba da zama a cikin wannan kwari, suna maraba da baki da hannu biyu biyu.


1  2  3  4