Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 16:07:59    
Ana sa ran cewa, Yi Jianlian zai shiga cikin hadaddiyar gasa ta NBA

cri

Tashar internet ta hadaddiyar gasar NBA ta kiyasta cewa, a gun babban taron zaben sabbin 'yan wasa da za a yi, za a mayar da Yi a matsayin lamba na 11, saboda shi babban mai tsaron gaba ne, kuma kungiyar wasan kwallon kwando ta Pistons ta Detroit za ta zabe shi. Ban da wannan kuma, tashar nan ta yi nazarin cewa, mai yiwuwa ne Yi zai kyautata kansa kamar yadda Paul Gasol na kungiyar Grizzlies ta Memphis ko kuma Dirk Nowitzki na kungiyar Mavericks ta Dallas suke. Yana da cikakkiyar kwarewa wajen yin wasan kwallon kwando, yana da kuzari sosai. Ya kan yi gasa kamar yadda 'yan wasan Amurka su kan yi.

Yanzu saura watanni misalin 8 da hadaddiyar gasar NBA ta fara babban taron zaben sabbin 'yan wasa na shekarar 2007, idan Yi yana son daga matsayinsa a gun babban taron zaben sabbin 'yan wasa, yana son shiga cikin hadaddiyar gasar NBA lami lafiya, to, tabbas ne ya gwada gwanintarsa daga dukan fannoni a nan gaba, kamar a gun taron wasannin motsa jiki na Asiya da za a yi a Doha a watan Disamba na wannan shekara. Yanzu ana horar da kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin da ke kunshe da Yi Jianlian a nan Beijing, Mr. Jonas ya bayyana cewa, yana fatan Yi Jianlian zai yi fintikau don kasarsa da kuma kansa a Doha. Ya ce,'Ina ganin cewa, da farko dai ya kamata ya mayar da moriyar kungiyar kasar Sin a gaban kome, ya yi la'akari da yadda zai taimaki kungiyar kasar Sin da ta zama lambawan. Idan kungiyar kasar Sin ta sami maki mai kyau, kuma ya ba da babbar gudummawa, to, ko shakka babu za a inganta matsayinsa a gun babban taron zaben sabbin 'yan wasa.'

Ko Yi Jianlian zai iya wasan kwallon kwando a cikin hadaddiyar gasar NBA a lokacin gasar wasa na gaba, idan ya sami dama, ko zai iya dasa harsashi yadda ya kamata a cikin irin wannan hadaddiyar gasa ta koli a duniya, ko zai iya zama Yao Ming na gaba ko a'a, to, za mu zura ido a kansa yau da watanni 8 masu zuwa.(Tasallah)


1  2  3