Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 16:07:59    
Ana sa ran cewa, Yi Jianlian zai shiga cikin hadaddiyar gasa ta NBA

cri

Bayan jin labari game da Yi Jianlian, babban malami mai horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Jonas Kazlauskas da kuma Wang Zhizhi, wanda shi ne dan wasa na farko na kasar Sin da ya shiga cikin hadaddiyar gasa ta NBA sun nuna masa fatan alheri, Mr. Jonas ya ce,'Ina fatan kome zai yi dai dai a gare shi. Ina ganin cewa, ya kamata ko wane dan wasa ya samar wa kansa wani babban buri, kuma ya yi kokari don tabbatar da shi. Bugu da kari kuma, irin wannan babban buri zai sa kaimi kansa da ya rubanya kokari da kuma mai da hankali a kan horo. Shi ya sa, a ganina, idan 'yan wasa matasa suna sa ran alheri domin shiga babban taron zaben sabbin 'yan wasa a cikin shakaru 2 zuwa 3 masu zuwa, to, wannan zai kawo wa makomarsu alheri.'

Wang Zhizhi ya ce,'Yin takara a cikin hadaddiyar gasar NBA zai kawo wa Yi Jianlian alheri wajen ci gabansa, ina fatan zai kara samun ci gaba.'

A cikin dukan 'yan wasan kasar Sin da ke aiki a cikin hadaddiyar gasar NBA, babu shakka Yao Ming na kungiyar Rockets ta Houston ya fi samun nasara, shi ne kuma daya daga cikin nagartattun 'yan wasan tsakiya a cikin hadaddiyar gasar NBA a halin yanzu. Yao Ming shi ma ya ji farin ciki sosai saboda Yi zai shiga babban taron zaben sabbin 'yan wasa.

Kafofin yada labaru na kasar Amurka suna ganin cewa, Yi Jianlian zai zama babban mutum a cikin hadaddiyar gasar NBA a shekarar 2007, sun mayar da shi tamkar Yao Ming na gaba, sun yaba masa sosai.

Bayan da Yi ya tabbatar da shiga babban taron zaben sabbin 'yan wasa na shekarar 2007, wani batu daban da ke jawo hankulan mutane shi ne ko Yi zai zama kan gaba a kan takardar sunayen sabbin 'yan wasa da za a zaba ko a'a. Game da wannan kuma, mataimakin babban manajan kungiyar Hongyuan ta Guangdong Liu Hongjiang ya nuna babbar aniya ya ce, dalilin da ya sa Yi bai shiga babban taron zaben sabbin 'yan wasa na shekarar 2006 ba shi ne domin ba a share fage sosai ba, amma yanzu kungiyarsa ta shirya sosai.


1  2  3