Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 16:07:59    
Ana sa ran cewa, Yi Jianlian zai shiga cikin hadaddiyar gasa ta NBA

cri
A kwanan baya, shahararren dan wasa Yi Jianlian na kasar Sin ya tabbatar da shiga babban taron zaben sabbin 'yan wasa da hadaddiyar gasar wasan kwallon kwando na Amurka wato NBA za ta shirya a shekara mai zuwa, akwai matukar yiwuwa cewa, zai zama dan wasa na hudu na kasar Sin da zai fara wasan kwallon kwando a cikin wannan hadaddiyar gasar wasan kwallon kwando ta koli, bayan abokan wasansa na kasar Sin Wang Zhizhi da Bateer da kuma Yao Ming.

Ko da yake shekarunsa ya kai 19 kawai, amma Yi Jianlian ya yi suna a rukunin wasan kwallon kwando na duniya. Ya fara jawo hankalin duniya saboda nagartacciyar baiwarsa a fannin wasan kwallon kwando a lokacin da ya kai 13 da haihuwa. Wannan sarauyi ya taba wakiltar kasar Sin wajen yin takara a cikin wasu muhimman gasannin wasan kwallon kwando na duniya, ya kuma sami maki mai kyau.

A 'yan kwanakin nan da suka wuce, kungiyar wasan kwallon kwando ta Hong Yuan ta lardin Guangdong ta bayyana ra'ayinta a hukunce, inda ta nuna cewa, ta yarda Yi Jianlian da ya shiga babban taron zaben sabbin 'yan wasa da hadaddiyar gasar NBA za ta shirya, saboda haka Yi Jianlian zai sami damar kyautata gwanintarsa a cikin hadaddiyar gasar wasan kwallon kwando ta matsayin koli a duk duniya.


1  2  3