Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-14 15:56:32    
Shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan da ke birnin Wuhan

cri

'Na yi shekaru gomai ina aiki a birnin Wuhan, yayin da na yi bako, na kan yi rakiyar abokaina ziyarar wuraren shakatawa da ke kusa da Wuhan. Wannan ne karo na 3 a gare ni. Akwai duwatsu da koguna a wannan shiyya, na ji dadi kwarai.'

Bayan sauka daga dutse na Mulan, mutane sun tuki mota har tsawon kilomita fiye da 10, su isa wurin shakatawa na dan tabki na Mulan. Wani babban kwari mai tsawon kilomita 10 ya tashi daga cikin tsaunuka 2, ya kuma hada tabkuna 2, wani babba da wani karami. Ruwansu na da tsabta, har mutane ba su son koma gida.

A cikin kwarin, magangarar ruwa da tabkuna da duwatsu da bishiyoyi masu ban mamaki suna ko ina, har ma mutane suna tsammani cewa, sai Allah ne kawai ya iya samar da wadannan wurare masu ni'ima.

Wuraren shakatawa da yawa masu hallayen musamman suna maraba da masu yawon shakatawa a shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan.(Tasallah)


1  2  3