Dutse na Mulan wurin shakatawa ne mafi girma da kuma muhimmanci a shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan, fadinsa ya kai murabba'in kilomita 78. Tsayinsa ya kai mita fiye da 580 daga leburin teku kawai, amma hawan wannan dutse yana bukatar karfi. Duk da haka masu yawon shakatawa suna iya hawan dutsen a karkashin inuwar dimbin bishiyoyin da ke a gabobin hanya, a wani lokaci kuma ana yin iska mai sanyi, mutane sun ji dadi sosai. Wata malama mai suna Wu Yu da ke hawan dutse ta bayyana cewa,
'Na yi gumi da yawa har na jike yayin da na isa kololuwar dutsen, amma na ji dadi sosai, na ji farin ciki, ban ji gajiya ba.'
Dutse na Mulan yana da girma da kyan gani, duwatsu da ni'imtattun wurare masu ban mamaki suna ko ina a kansa. Don girmama jaruma Hua Mulan, ban da sunan wannan dutse, wasu wuraren shakatawa masu halin musamman suna da nasaba da labarun Hua Mulan. Masu yawon shakatawa masu yawa sun kawo ziyara a nan domin wadannan labaru. Wani mai yawon shakatawa mai suna Lv Song ya bayyana cewa,
'Lokacin da nake karami, na taba karanta wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Hua Mulan ta shiga soja' a cikin littafi, shi ya sa na kawo nan ziyara a wannan gami. A ganina, halin dutse na Mulan da kuma wurare masu ni'ima da ke kansa sun nuna bambanci da na saura. Suna da kyan gani, sa'an nan kuma, akwai duwatsu da kaburbura da yawa.'
Ban da dutse na Mulan, lambu na Mulan shi ma ya yi suna. Wani itacen furen magnolia mai shekaru fiye da 1000 da haihuwa yana zama a cikin lambu na Mulan. Tsayinsa ya kai mita 10 ko fi, yana zama lami lafiya, an ce, Hua Mulan ita ce ta dasa wannan itace da kanta. A cikin watan Maris zuwa na Afril na ko wace shekara, furannin magnolia masu launin jar wur da yawa sun yi toho. Wani malam mai suna Wang Bin ya kan yi yawon shakatawa a nan kullun, bugu da kari kuma, ya kan jagoranci abokansa ganin wurare masu ni'ima a nan. Ya ce,
1 2 3
|