Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-14 15:56:32    
Shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan da ke birnin Wuhan

cri

Yanzu bari mu gabatar muku da wata shiyyar wurare masu ni'im da ke arewa maso gabashin birnin Wuhan, babban birnin lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin, wadda mazaunan wurin suka mayar da ita tamkar lambun da ke bayan birni, sunanta Mulan.

Saboda tana dab da tsaunukan Dabie, shi ya sa akwai kyawawan duwatsu da koguna da kuma kwaruruwa a cikin shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan. Musamman ma a lokacin zafi, zafin wurin bai fi na birnin Wuhan ba har digiri 5 zuwa 7, shi ya sa 'yan birni su kan zo wannan shiyya don gudun zafi.

Fadin shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan ya kai murabba'in kilomita 750, akwai wurare masu ni'ima manya da kanana fiye da 100, amma sunayensu suna da nasaba da Mulan, donme ake kira wannan shiyya da Mulan?

Dalilin da ya sa hakan shi ne wurin gari ne na wata jarumar zamanin da ta kasar Sin, sunanta Hua Mulan. Almara game da ita tana bazuwa a kasar Sin. A cikin zamanin daular Han na kasar Sin wato kafin shekaru fiye da dubu 2 da suka wuce, kananan kabilun da ke arewacin kasar Sin sun kutsa kai cikin yankin daular Han, shi ya sa gwamnatin daular Han ta daukar sojoji daga fararen hula don kare bakin iyakokin kasar, ko wane iyali ya tura wani namiji. Hua Mulan ta maye gurbin babbanta wanda ya tsufa da kuma karamin dan 'uwanta, ta sanya tufafi kamar yadda maza suke yi, ta shiga cikin soja. Ta yi shekaru 12 tana kare bakin iyakar kasar. A maimakon tona asirinta, an nada ta a matsayin kwamanda saboda cin nasara da yawa. Bayan yaki kuma, Hua Mulan ta yi murabus, ta koma gida don ciyar da iyayenta. Zuriyoyin mutanen garin Hua Mulan sun yi alfahari domin nagartaccen halin wannan jaruma, wato kishin kasa da kuma girmama iyaye. A sakamakon haka ne an yi wa wurare da kuma ni'imtattun wurare na wurin da sunan Hua Mulan.


1  2  3