Sa'an nan kuma, gwamnatin kasar Iran ta nemi gwamnatin Iraki da ta kashe Saddam. A shekarar 1980, Saddam Hussein ya ta da yakin da aka shafe shekaru 8 ana yinsa a tsakanin Iraki da Iran. Yawan mutanen kasar Iran da suka mutu a cikin yakin ya kai fiye da miliyan 1, an kuma lalata tattalin arzikin kasar Iran kwarai. A waje daya kuma, kasar Iran ta dade tana goyon bayan jam'iyyun siyasa na rukunin Shiite na kasar Iraki, kuma tana tuntubar muhimman jam'iyyun siyasa na Iraki na yanzu sosai. sakamakon haka, kasar Iran tana yin tasiri ga gwamnatin Iraki ta yanzu kwarai da gaske. A ran 7 ga wata, kakakin shugaban kasar Iran ya bayar da wata sanarwa, inda ya nemi gwamnatin Iraki da ta tabbatar da yanke hukuncin kisa kan Saddam domin magance kaucewa daga kisa.
'Yan kallo sun bayyana cewa, muhimmin dalilin da yake kawo illa ga aikin aiwatar da hukuncin da aka yi shi ne, saurin sake yin shari'ar Saddam da kotun daukaka kara ta Iraki za ta yi. Bisa ka'idojin dokokin kasar Iraki, ba za a iya kayyade saurin yin shari'a na kotun daukaka kara ba. Kotun daukaka kara za ta iya yin shari'ar Saddam da mabiyansa har na tsawon wasu watanni ko fiye. Bugu da kari kuma, har yanzu ba a sani ba ko kotun daukaka kara ta Iraki za ta jira sakamakon shari'a na matsalar Anfal da ake yi yanzu. Amma a ran 7 ga wata, malam Nuri al-Maliky, firayin ministan kasar Iraki ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne za a rataye Saddam Hussein kafin karshen wannan shekarar da muke ciki. Wannan maganar da malam Maliky ya yi ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Iraki ta yanzu ba za ta yarda da a jinkirtar da tsawon lokacin yin shari'ar ba. Mai yiyuwa ne za ta matsa wa babbar kotu lamba da ta kawo karshen shari'ar batun Anfal tun da wuri domin a iya kashe Saddam Hussein ta hanyar rataya tun da wuri. (Sanusi Chen) 1 2 3
|