
A ran 8 ga wata, ko da yake babbar kotun Iraki ta ci gaba da yin shari'a kan Saddam Hussein, tsohon shugaban kasar Iraki da manyan mabiyansa guda 6 kan batun Anfal, amma wasu 'yan kallo suna ganin cewa, koma mene ne sakamakon shari'a da ya faru kan Saddam, ba zai iya kaucewa daga kisa ba. Me ya sa aka fadi haka? Domin da farko dai, wannan kotu ta riga ta yanke hukuncin kisa kan Saddam ta hanyar ratayawa domin laifin da aka zarge shi a kai na yin yaki da dan Adam a cikin rikicin kauyen Dujail. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Iraki ta yanzu tana tsayawa kan matsayinta na kashe shi.
'Yan kallo sun nuna cewa, dalilan da suka sa gwamnatin Iraki wadda ke cikin hannun rukunin Shiite take tsayawa kan matsayin kashe Saddam su ne, da farko dai, wannan fatan jama'a ne.
1 2 3
|