Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-09 20:38:30    
Gwamnatin Iraki: Dole ne a kashe Saddam Hussein

cri

Yawan musulmi na rukunin Shiite da mutanen kabilar Kurd ya kai kashi 80 daga cikin kashi dari na dukkan yawan mutanen kasar Iraki. Lokacin da Saddam Hussein yake mulkin kasar Iraki, an danne su sosai. Sabo da haka, yanzu suna da kwadayin neman ramuwar gayya. Har wasu mutanen rukunin Shiite sun nemi a rataye Saddam a wani filin jama'a, kuma a watsa wannan labari ta gidan talabijin kai tsaye. Idan gwamnatin da ke karkashin jagorancin Nuri al-Maliky ta yi wa Saddam ahuwa, tabbas ne za ta gamu da haushi da rashin amincewa daga mutanen rukunin Shiite da na Kurd. Halin da ake ciki a kasar Iraki ma zai kara tabarbarewa.

Sa'an nan kuma, rukunin Shiite da jam'iyyun Kurd suna rike da ragamar mulkin gwamnatin Iraki tare. Lokacin da Saddam yake kan mukamin mulkin kasar Iraki, ya taba gana wa shuganninsu azaba sosai. Bugu da kari kuma, gwamnatin Maliky tana ganin cewa, idan za a iya kashe Saddam tun da wuri, hakan, zai amfana wa yunkurin yin yaki da dakarun rukunin Sunni wadanda suke da hulda da jam'iyyar Arab Baath Socialist, kuma zai amfana wa aikin tabbatar da kwanciyar hankali a kasar Iraki.

A waje daya kuma, a idon kasar Amurka, yanzu Saddam Hussein ba shi da amfani, wani wofi ne kawai. Yawancin kafofin watsa labaru na Larabawa suna ganin cewa, dalilin da ya sa babbar kotun Iraki ta yanke hukuncin kisa kan Saddam Hussein kafin ranar yin zaben wasu 'yan majalisun wakilai da dattawa na Amurka shi ne, tana son biyan bukatun shirin zabe na jam'iyyar Republican, wato jam'iyyar da shugaba George W. Bush na kasar Amurka yake ciki domin tabbatar da cewa, yakin Iraki da kasar Amurka ta yi yana da adalci. Amma yanzu, an riga an gama aikin zaben majalisun dokokin kasar Amurka, jam'iyyar Republican ta sha kaye a cikin zaben. Sakamakon haka, a ganin gwamnatin Amurka, yanzu, Saddam Hussein ba shi da amfani a gare ta.


1  2  3