Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 20:53:35    
Hasumiya ta Yueyang da kuma tsibiri na Junshan

cri

An binne su a kan tsibiri na Junshan. Har zuwa yanzu kabarinsu yana kasancewa a nan, an kuma gina dakin tunawa da su. Saboda labarin soyayya da kuma gorori tare da dige-dige, shi ya sa ana kira tsibiri na Junshan tsibiri ne na soyayya.

Ban da wannan kuma, wani irin shayi mai suna shayin Junshan da ake samarwa a tsibirin yana da ban mamaki, saboda yana mikewa tsaye a cikin ruwa mai zafi kamar yana rawa. Shayin Junshan na daya daga cikin manyan shahararrun shayi iri-iri guda 10 na kasar Sin, kuma yana daya daga cikin manyan shayi iri-iri guda 10 masu tsada na kasar Sin, a kan sami irin wannan shayi kadan ne a ko wace shekara.

Kunkuran da ke bayansu mai launin zinari suna zama a kan tsibiri na Junshan, suna jawo hankulan masu yawon shakatawa sosai. Saboda bayansu na musamman, shi ya sa ana kiransu kunkurai na zinari. Akwai wata almarar cewa, sun iya kawo wa mutane alheri. An ce, in wani ya tabo bayan irin wannan kunkuru, zai sami rai mai dogo; in ya tabo kansa, zai ba shi ruwa a duk ransa. Saboda haka, a lokacin da suke ziyarar wannan tsibiri, masu yawon shakatawa su kan tabo kyawawan wadannan kunkurai.(Tasallah)


1  2  3