Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 20:53:35    
Hasumiya ta Yueyang da kuma tsibiri na Junshan

cri

'

Na taba ziyarar hasumiya ta Yueyang sau da yawa, na fahimci abubuwa iri daban daban a duk lokacin da nake ziyararta. Kariyar katako iri ta kasar Sin da aka sassaka wata shahararriyar waka mai suna wakar hasumiyar Yueyang a kanta ta burge ni sosai. Ina tsammani zan iya yin yini daya ina jin dadin kallon wannan rubutu na kasar Sin da ke kan wannan kariya. Sa'an nan kuma, ni'imtattun wurare suna da kyau, na ji farin ciki saboda tsohon ginin mai kyan gani da kuma babban tabki na Dongting.'

A cikin tabki na Dongting akwai wani karamin kyakkyawan tsibiri mai suna Junshan, wani abin alfahari ne daban na birnin Yueyang. Fadinsa bai kai musarabba'in kilomita 1 ba, ya sha bamban da saura domin abubuwa 3 masu ban mamaki, wato gororin da suka iya yin hawaye, da ganyaen shayin da suka iya rawa, da kuma kunkuran wadanda bawonsu masu launin zinari.

Gororin da suka iya yin hawaye gorori ne na musamman da ke zama a kan tsibiri na Junshan, sunansu na gaskiya shi ne gorori masu dige-dige. Sun sha bamban da wadanda muka gani a yau da kullun, ana kasancewa da dige-dige masu ruwan kasa a jikunansu. An ce, wadannan dige-dige alamun hawaye ne. Wata budurwa na wurin mai suna Zou Liang ta yi karin haske cewa,

'Kafin shekaru fiye da dubu 4, 'ya'ya mata 2 na sarkin kasar Sin na zamanin da Yao sun auri sarki Shun, mai gadon sarkin Yao, amma sarki Shun ya rasu a kan hanyar rangadin aiki a kudancin kasar, wadannan mata 2 sun sami labarin rasuwar sarki Shun a yayin da suka isa tsibiri na Junsha, sun ji bakin ciki sosai, bayan da suka yi kwanaki 3 suke kuka tare da runguma gorori, sun jefa kansu a cikin ruwa saboda soyayya, hawayen da ke kan gororin sun zama dige-dige, wadanda ba a iya goge su ba.'


1  2  3