Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 13:46:38    
Masana'antun kasar Sin sun yi magunguna a kasashen Afrika

cri

Wannan karo na farko ne da masana'antun kasar Sin suka bayar da kudin tallafi ga daliban kasashen Afrika wajen ba da ilmi da aiwatar da harkokin ilmi. Wannan ya sami yabo sosai daga wajen rukunoni daban daban na kasar Kenya. A watan Afril na shekarar da muke ciki, a lokacin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara a kasar Kenya, an mayar da aikin nan a cikin tsarin yin hadin guiwar ba da ilmi a tsakanin kasashen biyu da kuma aiwatar da shi tamkar yadda aiwatar da sauran ayyukan gwamnati.

Lokacin da Mr Lu Chunming ya amsa tambayar da manema labaru suka yi masa dangane da sakamakon da kamfaninsa ya samu a kasashen Afrika, ya karfafa cewa, dole ne masana'antun kasar Sin su girmama al'adun kasashen Afrika da kuma kara fahimtar al'adunsu, wannan ne na da muhimmanci sosai. A ganinsa, dalilin da ya sa kamfaninsa ya sami sakamako mai kyau a kasashen Afrika shi ne saboda farashin maganinsa na da arha tare da inganci sosai, kuma kamfaninsa ya girmama al'adun kasashen Afrika sosai.Ya bayyana cewa, a hakika dai ne tushen yin cinikayya a tsakanin kasa da kasa shi ne fahimtar al'adunsu da girmama su.

Mr Lu Chunming ya bayyana cewa, a ganisa, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta riga ta sami bunkasuwa har zuwa wani sabon mataki a tarihi, wannan yana da amfani ga masana'antunmu wajen shiga kasuwannin kasashen Afrika da kuma yin hadin guiwa da ke tsakanin masana'antunmu da na kasashen Afrika.(Halima)


1  2  3