Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 13:46:38    
Masana'antun kasar Sin sun yi magunguna a kasashen Afrika

cri

Magani mai suna "Cotecxin", maganin kasar Sin ne da ya yi suna sosai a kasashen Afrika. A nahiyar Afrika, ana kiransa da cewa, abu ne mafi kyau da ke iya shawo kan cutar zazzabin cizon sauro. A cikin shekaru goma da suka wuce har zuwa yanzu, jama'ar Afrika suna karbe shi sosai saboda yana da arha da ingancinsa, ya ba da gudumuwa sosai ga jama'ar kasashen Afrika wajen kawar da rashin lafiya da suka samu bisa sakamakon zazzabin cizon sauro. Wani wakilin gidan rediyo kasar Sin ya ziyarci kamfanin harhada magunguna mai suna Cote da ke yin maganin Cotecxin na kasar Sin, yanzu ga abubuwan da wakilinmu ya ruwaito mana.

Bisa kididdigar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta yi, an ce, a kowace shekara, yawan mutanen Afrika da suke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ya kai kashi 90 cikin dari bisa na duk duniya, yawan mutanen da suka mutu bisa sanadiyar nan ya kai miliyan 3 ko fiye. Amma karfin magungunan gargajiya da aka yi amfani da sun riga sun ragu sosai. A shekarar 1993, magani mai suna "Cotecxin" da kasar Sin ta yi kuma kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta amince da shi ya shiga cikin kasashen Afrika, daga nan sai ake soma yin amfani da maganin "cotecxin" don shawo kan cutar zazzabin cizon sauro. Babban manajan kamfanin harhada magunguna mai suna Cote na birnin Beijing na kasar Sin Lu Chunming ya bayyana sakamakon da aka samu wajen yin amfani da magani mai suna "Cotecxin" a kasashen Afrika wajen shawo kan cutar zazabin cizon sauro, ya bayyana cewa, a farkon lokacin da na shiga kasashen Afrika, na yi zama a kasashen Afrika cikin dogon lokaci. Ni kaina na iya ganin amfanin maganinmu da aka yi a kasashen Afrika, kuma an amince da ingancinsa , a gaskiya ne maganin ya iya ceton mutane da yawa, kai, wannan shi ne abu mai kyau sosai gare ni.


1  2  3