
Jaridar Temes ta kasar Britaniya ta bayar da wani bayanin da aka rubuta cewa, magani mai suna Cotecxin" magani ne da ke da karfin dodo, ya ceci mutanen Afrika da yawansu ya kai miliyoyi.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lokacin da shugabannin kasar Sin sun kai ziyara a kasashen Afrika, ba sau daya ba ba sau biyu ba sun mayar da maganin Cotecxin don ya zama kyaututuka masu daraja sosai ga kasashen da suka kai ziyara.
A shekarar 2005, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya taba sanar da cewa, a shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta kara samar da agaji ga kasashen Afrika da kuma samar musu da magungunan da ke kunshe da maganin shawo kan cutar zazzabin cizon sauro da kuma samar musu taimakon kara kyautata gine-ginen asibitoci da horar da masu aikin jiyya.
Kamfanin Cote ya kuma tsai da kuduri na yin hadin guiwa da jami'o'I na kasashen Afrika, Mr Lu Chunming ya bayyana cewa, mun tsai da kudurin yin hadin guiwa da jami'ar Moi da jami'ar Nairobi na kasar Kenya, za mu zabi dalibai da yawansu ya kai dari da suka koyon ilmin likitanci don horar da su a cikin shekaru 5 a jere.
1 2 3
|