Sakamako mafi girma da Zhu Xi ya samu shi ne, da farko, ya yi nasarar takaita ilmin ladabi. Game da ilmin ladabi, an bayyana cewa, shi ne muhimmin halin da ilmin falsafa na kasar Sin take ciki bayan karni na 12, shi ne kuma ci gaban da aka samu bayan bunkasuwar ilmin Counficius. Bayan da Counficius ya kafa ilmin Counficius a karni na 5 na kafin bayyanuwar Annabi Isa(A.S), sai ilmin ya sami bunkasuwa a cikin shekaru fiye da dubu, amma sa'anan kuma ya fara nuna alamar tabarbarewa a kai a kai, musamman ma bayan shigar da addinin Buddah a kasar Sin, 'yan mulki na dauloli daban daban na kasar Sin suna da bambancin ra'ayi, wato wasu sun nuna girmamawa ga addinin Buddah, wasu sun nuna adawa da ilmin Counficius, amma jama'a farar hula suna rungumi akidar Counficius da akidar Dao da addinin Buddah, tsirarrun masanan akidar Counficius su ne suka yada ingancin akidar Counficius kawai.
Zhu Xi ya yi gadon hasashen ladabi na tsofaffinsa, ya hada da ilmin Counficius da na Buddah da na Dao gu daya don su zama wani tsarin tunani da ke hada da halittu da zamantakewar al'umma da logic gu daya, wadanda suka zo daga bayansa sun ce , wannan ne ilmin Zhuzi ke nan. A wajen ilmin Zhuzi , ana ganin cewa, hasashe da iska su ne suka kago dukan abubuwan duniya, a duniyar da ake ciki, ba a iya raba hasashe da iska ba, wato iska shi ne danyen kyayyaki na dukan abubuwa, hasashe shi ne hakikanin abu da kuma ka'idojinsa da ake bi, amma a hakika dai ne, hasashe ya fito ne kafin fitowar iska, a fannin nan, Zhu Xi ya gabatar da cikakken tunanin falsafa da tabbatar da shi.
1 2 3
|