Ilmin Counficius shi ne ilmin falsafa na ginshiki na zamanin aru aru na kasar Sin. A gun tarihin bunkasuwarsa na shekaru fiye da dubu 2, wani mutumi mai suna Counficius ya ba da gudumuwa ga somawar ilmin, wani mutumi daban mai suna Zhu Xi shi ma ya ba da gudumuwarsa. Yau za mu bayyana wasu abubuwa dangane da Zhu Xi.
An haifi Zhu Xi a shekarar 1130, ya mutu a shekarar 1200. An ce, shi ne babban mutumi da ke da tunani da ilmi sosai a kasar Sin bayan Counficius. Gidansa wani gida ne na bokayen gargajiya, kodayake ya kan fama da talauci, amma tun lokacin da yake karami, ya sami tarbiyya sosai daga wajen ilmin Counficius. Sa'anan kuma, bayan mutuwar mahaifinsa, sai Zhu Xi ya bar garinsa da ke lardin Jiangxi na kasar Sin zuwa Wuyishan na lardin Fujian don ci gaba da samun tarbiyya dangane da ilmin Counficius.
A lokacin da ya cika shekaru 19 da haihuwa, ya shiga jarrabawa don neman samun mukamin gwamnati, sa'anan ya shiga cikin rukunin jami'an gwamnati bisa sakamakon jarrabawa mai kyau da ya samu. Amma, a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, ayyukan gwamnati ba su da yawa gare shi, shi ya sa ya sami dama sosai wajen wallafa littattafai da kuma ba da lacca ga dalibai.
1 2 3
|