Jakada Wu Sike ya ci gaba da cewa, kasashen biyu dukansu suna mai da hankali ga raya al'adu, a sa'I daya kuma, dukansu suna tsayawa tsayin daka don yin shawarwari a tsakaninsu bisa bambancin wayin kai da kuma yin ma'amala a tsakaninsu, ba su amince da ra'ayin yin hargitsi bisa bambancin wayin kai da ke kasancewa a tsakaninsu. Saboda haka har wa yau dai kasashen biyu suke yin ma'amala a tsakaninsu cikin himma da kwazo.
Jakada Wu Sike ya gaya wa manema labaru cewa, shugaban kasar Masar Mubarak zai halarci taron koli na yin dandalin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wanda za a kira a nan gaba ba da dadewa ba.Ya kuma bayyana cewa, shugaba Mubarak zai kai ziyarar aiki a kasar Sin.(Halima) 1 2 3
|