A cikin shekaru 50 da suka wuce, abubuwan da aka yi a tsakanin kasar Sin da kasar Masar wajen yin hadin guiwar sada zumunta suna ta kara wadatuwa. A shekarar 1999, bangarorin biyu sun sami ra'ayi daya wajen kulla huldar abokantakar yin hadin guiwa bisa manyan tsare-tsare. A lokacin da aka maraba da zuwan ranar cika shekaru 50 da kullar huldar diplomasiya a tsakaninsu, ziyarar farko da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi a kasar Masar tare da nasara ta sa kaimi ga shigar da huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Masar cikin wani sabon mataki. Wajen harkokin siyasa, kasar Sin da kasar Masar suna amincewar juna bisa zaman daidai wa daida, wajen yin harkokin tattalin arziki da cinikayya, kasashen biyu suna neman samar wa juna moriya iri daya tare da samun nasara gu daya. Jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Masar Wu Sike ya bayyana mana wani misali, ya ce, a duk lokatan da firayim ministan kasar Masar Ahmed Nazif ya gana da kungiyoyin wakilan kasar Sin sau da yawa, ya bayyana cewa, lokacin da ya dau nauyin mukamin ministan sadarwa, ya soma hadin guiwar sadarwa da kamfanonin kasar Sin, a wancan lokaci, kasar Masar ta fahimci fasahohin fannin nan na kasar Sin kadan ne ba da yawa ba, mutane da yawa sun yi shakkar makomar hadin guiwar nan. Bisa matsayina na ministan kasar Masar, na nace ga yin hadin guiwa da kasar Sin, sa'anan kuma hakikanan abubuwa sun shaida cewa, na yi nasara, wannan yana da amfani ga hanzarta kasar Masar wajen samun bunkasuwa a fannin nan, kuma ya zama wata dama ga masana'antun kasar Sin.
1 2 3
|