Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-17 17:36:20    
Kasar Sin da kasar Masar su ne abokai masu kirki kuma aminai da 'yanuwa masu kirki a tsakaninsu

cri

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 50 da soma kulla huldar jakadanci a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.Don kara dankon zumuncin gargajiya da kara inganta hadin guiwar sada zumunta da ke tsakanin bangarorin biyu, sai bangarorin biyu wato Sin da kasashen Afrika za su shirya taron koli na Beijing na dandalin yin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wato taron ministoci na uku. Game da wannan, wakilan gidan rediyon kasar Sin ya kai ziyara a ko'ina a kasashen Afrika da kuma ziyarci mutane na rukunoni daban daban. Yau za mu karanta wani bayanin musamman da wakilanmu suka rubuta mai lakabi haka: Kasar Sin da kasar Masar su ne abokai kuma aminai da 'yanuwa masu kirki a tsakaninsu.

A ranar 30 ga watan Mayu na shekarar 1956, kasar Masar ta kulla huldar jakadanci da Jamhuriyar jama'ar Sin da ke kafuwa ba da dadewa ba , shi ya sa ta zama ta farko ta kasashen Larabawa da kasashen Afrika da ke amincewa da sabuwar kasar Sin. Lokacin da jakadan kasar Sin da ke wakilci a kasar Masar Wu Sike ya tabo magana a kan tarihin nan, ya gaya wa manema labaru cewa, kullar huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasar Masar shi ne wani al'amari mai muhimanci a tarihin harkokin waje na kasar Sin, ana iya rubuta wannan a cikin littafin tarihin diplomasiya na kasar Sin. Kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasar Masar ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afrika da na Larabawa sun shiga wani sabon matakin tarihi. Saboda haka, lokacin da aka yi murnar ranar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasar Sin da kasar Masar shi ne ranar cika shekaru 50 da kasar Sin ta kulla huldar diplomasiya a tsakaninta da kasashen Afrika, kuma rana ce ta cika shekaru 50 da kasar Sin ta soma kulla huldar diplomasiya a tsakaninta da kasashen Larabawa.


1  2  3