Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-16 15:16:42    
An fara taron cinikin kayayyakin kasar Sin da za a fitar da su zuwa kasashen waje a karo na 100

cri

Bugu da kari kuma, Mr. Wen ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin cewa, tun daga shekara mai zuwa, wato taron fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje na 101 zai zama taron fici da shigin kayayyaki na kasar Sin. Mr. Zhang Wenyuan, shugaban wani kamfanin samar da fasahohin zamani na kasar Sin yana ganin cewa, idan an kwatanta shi da taron da ake yi yanzu, ko da yaka a kara kalma daya kawai a cikin sabon taron da za a yi, amma, wannan muhimmin sauyi ne irin na tarihi. Mr. Zhang ya ce, "Ba ma kawai an kara kalma daya kawai ba, har ma ana bayyana sauye-sauyen manufofin cinikin waje na kasar Sin. A da, kasar Sin tana bukatar kudaden kasashen waje. Sabo da haka, ta sa kaimi wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje domin neman wasu kudaden waje. Amma yanzu, ta riga ta samu bunkasuwar tattalin arzikinta kwarai, ya kamata mu shigar da kayayyakin kasashen waje, lokacin da muke ci gaba da fitar da kayayyakinmu. A waje daya kuma, wannan wata kyakkyawar manufa ce wajen kawar da kiki-kaka a fannin cinikin waje."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yawan ribar da kasar Sin ta samu a fannin cinikin waje yana ta karuwa. A shekarar da ta gabata, a karo na farko ne, adadin yawan ribar da kasar Sin ta samu daga wajen cinikin waje ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 10. Kwararru suna ganin cewa, taron fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje ya zama taron fici da shigin kayayyaki na kasar Sin, wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka lokacin da take aiwatar da manufofin moriyar juna da samun nasara tare da kasashen waje da kuma yunkurin cimma burin samun daidaito a tsakanin aikin fici da shigi. (Sanusi Chen)


1  2  3