Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-16 15:16:42    
An fara taron cinikin kayayyakin kasar Sin da za a fitar da su zuwa kasashen waje a karo na 100

cri

A ran 15 ga wata, an fara taron cinikin kayayyakin kasar Sin da za a fitar da su zuwa kasashen waje na karo na 100 a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin. A gun bikin kaddamar da taron, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, tarurukan cinikin kayayyakin kasar Sin da ake fitar da su zuwa kasashen waje sun taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da cinikin waje na kasar Sin gaba, shi kuma muhimmiyar alama ce ga yunkurin bude kofar kasar Sin ga kasashen waje. Haka nan kuma, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bin manufar bude kofarta ga kasashen waje da yin musanye-musanye da hadin guiwa da kasashen waje a nan gaba domin raya wata al'umma mai jituwa tare.

An fara yin taron fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje ne a Guangzhou ne a shekarar 1957. Ana shirya wannan taro har sau biyu a lokacin bazara da kuma lokacin kaka a birnin Guangzhou a kowace shekara. Sabo da haka, shi gaggarumin taro ne mafi girma inda ire-iren kayayyakin da ake ciniki suka fi yawa, baki 'yan kasuwa da suke zuwa taron ma suka fi yawa. Kuma tarihin irin wannan taro ya fi dadewa a na kasar Sin.


1  2  3