Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-16 15:16:42    
An fara taron cinikin kayayyakin kasar Sin da za a fitar da su zuwa kasashen waje a karo na 100

cri

Lokacin da yake ganawa da wakilinmu, malam Hashem Shahrestani, wani dan kasuwa daga kasar Iran ya bayyana cewa, taron fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje na Guangzhou ya samar wa baki 'yan kasuwa kamar shi damar yin kasuwanci da yawa. Malam Shahrestani ya ce, "Ana jin mamaki sosai domin ana shirya taron fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje na Guangzhou har sau dari 1. Na ji an ce, lokacin da aka fara shirya wannan taro a shekarar 1957, wani karamin taro ne. Amma yanzu ka ga ya zama wani taron cinikin kayayyaki mafi girma, kuma ana samun nasarar ciniki kwarai. Ba ma kawai Irin wannan taro ya sa kasar Sin ta samu moriya ba, hatta ma baki 'yan kasuwa kamar ni muna samun damar sayen kayayyakin kasar Sin."

A gun bikin taya murnar cikon shekaru 100 da kafuwar taron fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje na Guangzhou, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya ce, "Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bin manufar bude kofarta ga kasashen duniya. Kuma za mu bi ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO da kara bude wa kasashen waje kasuwanni da halartar aikin raya tsarin yin cinikin waje a tsakanin bangarori daban-daban da ake yi a duk duniya. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Sin za ta sa kaimi ga yunkurin zuba wa juna jari a tsakanin Sin da kasashen waje, kuma da kyautata ingancin yin amfani da jarin waje."


1  2  3