Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-02 18:33:23    
Bunkasuwar kasar Sin ya samar da abin koyi ga Afirka

cri

Lokacin da ya tabo magana a kan huldar da ke tsakanin Masar da Sin kuma, Mr.Abu Gheit ya ce, Masar kasar Afirka ce ta farko da ta kulla huldar diplomasiyya tare da jamhuriyar jama'ar Sin. Shekarar da muke ciki kuma shekara ce ta cikon shekaru 50 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, a cikin shekaru 50 da suka gabata, kasashen biyu sun mara wa juna baya, kuma sun bai wa juna taimako, huldar da suka kulla a tsakaninsu tamkar irin ta 'yan uwa ne. Mr.Abu Gheit ya kuma kara da cewa, bunkasa da kuma inganta huldar hadin gwiwa a tsakanin Masar da Sin babban buri ne da Masar ke neman cimmawa a wajen manufarta ta diplomasiyya.

A shekara ta 1999, kasashen Masar da Sin sun rattaba hannu a kan wata hadaddiyar sanarwa dangane da kulla muhimmiyar huldar hadin gwiwa a tsakaninsu. Daga baya, a watan Yuni da ya gabata, bangarorin biyu sun kuma daddale tsarin ka'idoji dangane da zurfafa muhimmiyar huldar hadin gwiwa a tsakaninsu. Ban da wannan, bangarorin biyu sun kuma kulla wasu yarjejeniyoyi dangane da ciniki da zuba jari da dai sauransu, wadanda suka aza harsashi a fannin doka don bunkasa huldar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen biyu. A shekara ta 2005, yawan kudin cinikin da aka yi a tsakanin Masar da Sin ya kai dallar Amurka biliyan 2 da miliyan 150, wanda ya karu da kashi 36% bisa na shekarar 2004.

Daga karshe, Mr.Abu Gheit ya kuma tsamo maganar shugaban kasar Masar, Mr. Moubarak cewa, Sin da Masar dukansu suna daga cikin wadanda suka kawo tarihi mai girma da ci gaba ga dan Adam, kuma su ne suke tsaron tsofaffin kayayyakin tarihi na dan Adam, har kullum, suna neman cimma babban buri.(Lubabatu)


1  2  3