Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-02 18:33:23    
Bunkasuwar kasar Sin ya samar da abin koyi ga Afirka

cri

Mr.Abu Gheit ya kuma nuna yabo a kan shawarar da kasar Sin ta gabatar a shekara ta 2000 dangane da kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kuma a cewarsa, shawarar ta tabbatar da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Afirka da Sin a hakika. Kasashen Afirka da Sin za su yi amfani da taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wanda za a yi a farkon watan Nuwamba mai zuwa a nan birnin Beijing, don ci gaba da bunkasa huldar da ke tsakaninsu, musamman ma a fannin tattalin arziki da ciniki.

Mr.Abu Gheit ya ci gaba da cewa, ko a lokacin yaki da mulkin mallaka don neman 'yancin kan al'umma, ko kuma a lokacin da ake neman bunkasuwa bayan da aka samu 'yancin kan al'umma, har kullum dai, Afirka tana samun goyon baya daga jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Goyon bayan da kasar Sin ke nuna wa Afirka yana da muhimmancin gaske, kuma ya samu babban yabo daga gwamnatocin kasashe daban daban na Afirka da kuma jama'arsu.

Ban da wannan, a ganin Mr.Abu Gheit, babu wani abin da ya hana ruwa gudu a wajen bunkasa muhimmiyar huldar abokantaka ta sabon salo a tsakanin kasashen Afirka da Sin. Tabbas ne za a iya shiga cikin wani sabon zamani na sabuwar huldar abokantaka da ke tsakanin Afirka da Sin, da kuma kawo wa jama'ar Afirka da ta kasar Sin alheri, idan bangarorin biyu na Afirka da Sin su yi kokari tare, kuma su dauki hakikanan matakai, su inganta fahimtar juna da mu'amala a tsakaninsu ta hanyoyin gwamnati da kuma jama'a.


1  2  3