
Kwanan nan, Mr. Ahmed Ali Abul Gheit, ministan harkokin waje na kasar Masar, ya nuna yabo sosai a kan huldar da ke tsakanin Afirka da Sin. Ya ce, kasashen Afirka da Sin suna son kulla muhimmiyar huldar abokantaka ta sabon salo a tsakaninsu, kuma bangarorin biyu suna imani da cewa, tabbas ne irin wannan hulda za ta kawo musu nasarori tare.
Mr.Abu Gheit ya ce, game da bunkasa muhimmiyar huldar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Afirka da Sin, kasar Sin ta samar da abin koyi ga kasashe daban daban na Afirka a wajen inganta ciniki da fitarwa da kayayyaki zuwa kasashen waje, kuma kyawawan fasahohin kasar Sin za su bayar da babban tallafi ga kasashen Afirka.
1 2 3
|